Rasha ta ce za a iya warware rikicin Belarus
August 23, 2020Talla
Mr. Lavrov ya ambata hakan ne dazu yayin wani taron manema labarai da ya yi, inda ya ce lamura a kasar sun fara daidaituwa amma kuma a share guda ya ce irin matsayin da shugabar 'yar adawar kasar ta dauka kan halin da ake ciki sam baya kan tsari.
Ministan na harkokin wajen kasar ta Rasha ya ce kiran da ta yi na shugaban Belarus din ya sauka daga gadon mulki ba zai haifar da wani abu mai ma'ana ba illa jefa kasar cikin irin halin da Venezuela yanzu haka ta ke ciki.
Wadannan kalamai na Lavrov dai na zuwa ne bayan da dubban mutane da ke adawa da shugaban Belarus din suka fantsama kan titunan babban birnin kasar wato Minsk inda suka yi zanga-zanga ta kin jinin mulkinsa.