SiyasaTurai
Rasha ta ce da sauran tafiya kafin dakatar da yakin Ukraine
March 23, 2025Talla
Fadar mulkin Rasha ta Kremlin ta kawar da yiwuwar samun nasarar cimma yarjejeniyar dakatar da yakin Ukraine cikin hanzari, kasancewar tattaunawar sulhun ba za ta zo da sauki ba.
Karin bayani:Firaministan Burtaniya Starmer ya shiga wasiwasi kan Trump
Kakakin fadar Dmitry Peskov ya shaida wa gidan talabijin din kasar cewa yanzu aka fara ma shiga matakin farko na samar da masalahar, wadda Amurka ke jagoranta a kasar Saudi Arebiya da za dora ranar Litinin.
Karin bayani:Trump ya yi wa Ukraine tayin gudanar da ayyuka a tashoshin makamashin kasar
Amurka na fatan cimma matakin karshe na sulhun cikin makonni masu zuwa, a kalla nan da ranar 20 ga watan Afirilu 2025.