Rasha: A guji danganta batun Navalny da aikin gas zuwa Jamus
September 16, 2020Kakakin fadar mulki ta Kremlin a Rasha Dmitry Peskov ya ce bai kamata a danganta aikin shimfida bututun gas da ake wa lakabi da Nord Stream 2 da zai dakon gas daga Rasha zuwa Jamus da batun dan adawar Rashar nan Alexei Navalny ba.
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel a kwanakin nan tana tana shan kira da ta dakatar da aikin na shimfida bututun da yanzu haka aka kusa kallama shi, wanda zai samar da gas daga Rasha zuwa Jamus a matsayin martani ga gubar da aka saka wa mai sukar lamirin gwamnatin Rasha, Alexei Navalny, a watan da ya gabata.
Gwamnati a birnin Mosko ta ce har yanzu ba ta samu wata kwakkwarar shaidar da ke tabbatar da an sanya wa Navalny gubar da ke janyo sarkewar jijiyon jiki ba. Peskov ya jaddada cewa a shirye Rasha ta ke ta ba wa Jamus hadin kai a kan batun sai dai har yanzu bukatar Rashan ba ta sami karbuwa ba.