Rasha ta amince da daular Musulumcin Taliban a hukumance
July 4, 2025Rasha ta zama kasa ta farko da ta amince a hukumance da daular Musulumci da kungiyar Taliban ta kafa a kasar Afghanistan, matakin da fadar mulki ta Kabul ta jinjinawa matuka.
Tun da farko dai kakafin ma'aikatar harkokin wajen Afghanistan Zia Ahmad Takal ne ya sanar da wannan labari, kafin daga bisani ma'aikatar diflomasiyyar Rasha ta tabbar tare da cewa a karon farko an daga sabuwar tutar Afghanistan wadda 'yan Taliban suka samar a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Moscow.
Dama dai wasu majiyoyi sun ambato ma'aikatar harkokin wajen Rasha a ranar Alhamis na cewa kasar ta karbi sabon jakada da Afghanistan ta aike zuwa Moscow, sannan kuma fadar mulki ta Kremlin ta daura aniyar tallafa wa Kabul domin inganta harkokin tsaro da yaki da ta'addanci da kuma fataucin miyagun kwayoyi.
Karin bayani: MDD ta damu a game da sabbin dokokin da'a a Afganistan
Wannan mataki na Rasha na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Talliban ke neman samun karbuwa a kuma gayyato masu saka hannun jari bayan da kungiyoyi kasa da kasa da kuma kasashen duniya suka mayar da ita saniyar ware saboda matakai masu tsauri da ta dauka bayan dawowarta kan madafun iko a 2021.