SiyasaJamus
Rasha na zargin yi mata kutse
September 10, 2021Talla
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta gayyato jakadan Amirka da ke a kasar, domin yi mata bayani a game da wani kutse da ake zargin wasu kamfanonin fasahar Amirka ke yi a kan harkokin zaben kasar.
Nan gaba a cikin wannan watan na Satumba ne dai za a gudanar da zaben 'yan majalisar kasa a Rashar.
Kasar ta Rasha ta sake inganta makatan tsaro a bangaren sadarwar intanet dinta, da ma matakan shari'a a kan kamfanonin da ke kokarin yi mata kutse cikin rumbunanta na bayanai.
Takaddama dai na zafi a tsakanin Rasha da Amirka akan batutuwan da musamman suka shafi sa baki cikin harkokin zabe da kuma take hakkin bil Adama.