Shugaban Rasha Vladimir Putin ya soma rangadi a Austria
June 5, 2018Talla
Putin da ke ziyarar rangadi a yankin, ya soma sauka ne a birnin Vienna na kasar Austria daya daga cikin kasashen da ke da kyakyawar huldar diflomasiya da kasarsa. A wata zantawa da ya yi da kafar yada labaran kasar, ya ce yana neman hadin kan shugabanin kasashen EU amman kuma ya jadadda mahinmancin dangantakar kasarsa da Austria da ya kira babban aminiya.
Wannan ita ce ziyararsa ta farko tun bayan soma mulki a wa'adin na hudu. Rasha da sauran kasashen EU sun sami sabani a bisa rawar da kasar ta taka a rikicin Ukraine na marawa 'yan aware baya. Lamarin ya sa kasashen daukar matakin janye jakadunsu daga Rasha.