Rasha na nazarin shawara game da Syriya
February 13, 2012Ƙasar Rasha ta fara nazarin shawarar da ƙungiyar haɗin kan larabawa ta bayar a ranar lahadi, ta bin hanyoyi na dipolomasiya wajen sulhunta rikicin Siyasa ta ƙasar Syriya . Ministocin harkokin waje na ƙasashen larabawa sun sanar da wasu jerin hanyoyin da ya kamata a bi, domin kawo ƙarshen zub da jini a birnin Homs, waɗanda suka haɗa da turawa da rundunar haɗin guywa da za ta wanzar da zaman lafiya a ƙasar Syriya.
Ministan harkokin wajen Rasha Serguei Lavrov ya nunar a birnin Moscow cewar akwai bukatar tsagaita wuta tsakanin dakarun gwamnatin Bashar al-Assad da kuma masu fafutukar tabbatar da demokaraɗiya , idan ana so a gano bakin zaren warware rikicin na syriya.
Ita dai fadar mulki ta Damascus ta lashi takobin dawo da doka da oda a cikin ƙasar ta Syriya ta ko halin kaka. Yayin da su kuma 'yan adawan ke ci gaba da kokawa da matakan da gwamnati ke ɗauka, domin murƙushe boren da suka fara tun watannin 11 da uka gabata. A halin yanzu dai dakarun da ke biyeyya ga gwamnatin Bashar al-AAsad na ci gaba da luguden wuta a birnin Homs da ke zama cibiyar tayar da ƙayar baya ta Syriya.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh