Rasha: Mutane 64 suka halaka a gobara
March 26, 2018Mutane 64 ne suka halaka mafi akasari kananan yara bayan afkuwar wani bala'in gobara a katafaren shagon cefane na Siberia mai yawan masana'antu kamar yadda jami'an gwamnati suka bayyana a wannan rana ta Litinin, wannan dai na zuwa ne yayin da masu aikin agaji suka shiga zakulo gawarwaki karkashin baraguzan gini a inda lamarin ya afku.
Ministan ma'aikatar da ke lura da aiyukan agajin gaggawa Vladimir Puchkov ya bayyana cewa cikin mutanen 64 har da guda shida wadanda ke karkashin baraguzan gini suka halaka a gobarar.
Kafar yada labaran talabijin a kasar ta Rasha ta nuna hotuna yadda bakin hayaki ya turnike saman ginin katafaren shagon cefanen na Winter Cherry a birnin Kemerovo, babban shagon da a cikinsa akwai rukuni na shaguna daban-daban da wajen tausa da gidan kallo da ke cika da jama'a musamman a ranakun Lahadi da rana.