Kotu ta daure mabiyin addinin Jehovah a Rasha
November 6, 2019Talla
Kotun ta yanke hukuncin dauri ne bayan da ta samu mutuman mai suna Serguei Klimov dan shekaru 49 da haihuwa da kafa wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addini.
Tuni dai madugun 'yan adawar kasar ta Rasha Alexei Navalny ya soki lamirin hukuncin kotun yana mai zarginta da rufe mutanen a kan imaninsu da addininsu.
A watan Aprilun 2017 ne dai gwamnatin kasar ta Rasha wacce ta kunshi mabiya tafarkin na Jehovah sama da dubu 175, ta haramta gudanar da tafarkin na Jehovah a bisa zargin mabiyansa da yada tsattsauran ra'ayin addini.