Rasha da Ukraine za su sake hawa kan teburin sulhu
June 2, 2025Wakilan kasashen Rasha da Ukraine za su sake zama gaba da gaba a kan teburin sulhu a karo na biyu tun bayan fara yakin Ukraine a shekarar 2022. Sai dai har yanzu ana ganin akwai 'yar tazara a tsakanin bangarorin biyu kan yadda za a kawo karshen yakin. Ko a karshen mako, Ukraine ta kaddamar da sabbin hare-hare kan sansanonin sojin Rasha yayin da fadar Kremli ta harba jirage marasa matuka 472 zuwa Ukraine.
Karin bayani: Taron Rasha da Ukraine a Turkiyya
A zagayen farko na tattaunawar da ta gudana a ranar 16 ga watan Mayun wannan shekarar, an ga yadda ya kai ga musayar fursononi mafi girma, sai dai kuma babu wata alama ta zaman lafiya. Wakilin Amurka a tattaunawar, Keith Kellogg ya ce bangarorin biyu za su gabatar da takadar bayanai kan bukatunsu na tsagaita bude wuta.