Rasha da Ukraine za su daina far wa tashoshin makamashi
March 26, 2025Amurka ta cimma yarjejeniya da kasashen Rasha da Ukraine domin dakatar da farmakin da suke kai wa juna a kan teku da kuma wuraren makamashi.
Washington ta kuma amince da dage wasu daga cikin takunkuman da ta kakaba wa Moscow a sabuwar yarjejeniyar da ta sanar.
Ukraine da Rasha sun amince da tsagaita wuta a Bahar Maliya
Ko da ya ke ba a yi dalla-dalla kan yaushe da kuma yadda kasasahen za su dakatar da hare-haren ba amma dai yarjejeniyar ta kasance ta farko da aka kulla a hukumance tun fara shugabancin Donald Trump.
Yarjejeniyar da Amurkar ta sanar ta hada da taimaka wa Rasha a dage mata takunkuman kasa da kasa kan kayan gona da taki da kuma wasu abubuwa da take fitar wa zuwa kasaahsne ketare.
Rasha ta ce da sauran tafiya kafin dakatar da yakin Ukraine
To sai dai kuma shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce shi dai a fahimtarsa yarjejeniyar ba ta kunshi sakar wa Rasha mara ba inda ma ya ce Rasha na kokarin yin inda-inda a cikin abinda aka cimma na yarjejeniyar.