Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunonin yaki
August 14, 2025Talla
Kasashen Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunonin yaki 84 daga kowane bangare a wannan Alhamis, a jajibirin ganawar da Shugaba Vladimir Putin zai yi da takwaransa na Amurka Donad Trump a ranar Juma'a a birnin Alaska.
A cewar ma'aikatar tsaron Rasha dai tuni sojojin kowane bangare da aka saka, suka suka isa cikin dangi.
Kawo yanzu dai musayar fursunonin yaki da gawarwakin sojojin da suka kwanta dama a fagen yaki, ita ce nasara daya tilo da aka samu a tattaunawar da Turkiya da Amurka suka jagoranta da nufin warware rikicin Rasha da Ukraine wanda ya barke yau sama da shekaru uku da rabi.
Cikin watan Yuli da ya gabata, Rashar da Ukraine sun watse baram-baram a zaman da suka yi a Istanbul saboda sabanin ra'ayi a kan wasu muhimman batutuwa.