Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunoni
May 24, 2025Talla
Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine gami da ma'aikatar tsaron kasar Rasha sun yi musayar sojoji 307, kwana guda bayan duka bangarorin sun saki fararen hula 390.
A wata sanarwa da ya wallafa a kafar Telegram, shugaban Ukraineya ce suna fatan Rasha ta amince a ci gaba da musyar fursunonin don su sami damar komawa ga iyalansu.
Sama da shekaru uku ke nan kasashen Rasha da Ukraine dake makwabtaka da juna suka gwabza kazamin fada, inda a karon farko a watan Mayu jami'an bangarorin biyu suka gana a birnin Istanbul na Turkiyya domin lalubo hanyoyin maslaha na kawo karshen yakin, duk da cewar ba a yi nasara ba amma Moscow ta amince da musayar fursononi.
Karin Bayani: Taron Rasha da Ukraine a Turkiyya