Moscow da Kyiv na zargin juna da jinkirta musayar fursononi
June 7, 2025Ana dai ganin musayar fursunoni tsakanin Moscow da Kyiv a matsyin wani mataki da zai kai ga nasara a tattaunawar zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu. Tuni dai gwamnatocin na Kyiv da kuma Moscow suke zargin juna da jinkirtawa da kuma dakile musayar. Tsaiko ga musaya fursunoni da bangarorin biyu suka ce za a yi a karshen makon nan ya zo ne a daidai lokacin da sojojin Moscow suka kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka da bama-bamai a cikin dare, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 10.
Karin bayani: Rasha da Ukraine na musanyar fursunoni
A tattaunawarsu ta birnin Santanbul na kasar Turkiyya, Kyiv da Moscow sun amince su saki dukannin dakarunsu da suka ji rauni da kuma wadanda aka kama 'yan kasa da shekaru 25, wanda ya kai jimilyar mutane 1,000 daga kowani bangare. Sai dai kuma har yanzu bangarorin biyu ba su tsayar da takamanmiyar ranar musayar ba.