Rasha da Ukraine na musanyar fursunoni
May 23, 2025Rahotanni daga jami'an gwamnatin Ukraine, sun tabbatar da musayar fursunoni tsakanin kasar da Rasha, wannan na daya daga cikin alamun da ke nuna cigaba a yunkurin da manyan kasashen duniya ke yi na kawo karshen yakin shekaru tsakanin kasashen guda biyu.
A makon da ya gabata ne dai jami'an kasashen Rasha da Ukraine suka cimma yarjejenaiyar musanyar fursnunon yaki guda 1,000 daga kowane bangare, bayan ganawar farko da aka yi a birnin Santanbul na kasar Turkiyya.
EU za ta sake lafta wa Rasha takunkumai kan yakin Ukraine
Kungiyar Tarayyar Turai dai na zargin Shugaba Putin da jan kafa a kokarin sulhunta rikicin, sai dai Putin ya dade yana nuna bukatar Ukraine ta janye sojojinta daga yankuna hudu da ya mamaye a watan Satumban 2022 a matsayin sharudan fara samun zaman lafiya.