Rasha da Tarayyar Turai na inganta hulɗa
June 4, 2012Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya kare matakin kasar kan girmama hakkin bil Adama, yayin ganawa da Kungiyar Tarayyar Turai da ya gudana a kasar ta Rasha. Kuma dukkanin sassan sun amince da rohoto Kofi Annan zai taimaka wajen samun zaman lafiya cikin kasar Siriya. Suleiamn Babayo ya haɗa mana rohoto akai:
Shugaban na Rasha Vladimir Putin dake fuskantar matsin lamba daga ƙasashen Yammacin Duniya, ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu Rasha bata da 'yan fursunan siyasa, kuma da ya ke amsa tamboyoyi manema labarai yayin taron na birnin St Petersburg, ya ce dokokin ƙasar kan zanga zanga daidai suke dana sauran ƙasashen Turai.
Yayin taron Shugaba Putin ya nuna matsalolin shige da fice dake ci gaba da karar tsaye wa sassan biyu, inda ya bada misani da tsakaitacce visa shiga ƙasar Faransa da aka baiwa 'yan jaridun dake masa rakiya.
Ƙawance tsakanin zaiyi wuya idan aka duba matsalolin shige da fice, na neman izinin visa tsakaninmu, da ƙasashen yammacin Turai na zuwa Berlin ko Paris. 'Yan jaridun dake mun rakiya an basu visa na sa'oi 24 yayin ziyara zuwa Faransa, idan aka samu makara wajen gudanar da taron da aka tsara mai zai kasance matsayin su ke nan.
Ranar Jumma'a data gabata Shugaba Vladimir Putin na Rasha da Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun tattauna kan rikicin Siyasa, kuma Putin ya yi karin haske.
Makaman da Rasha take sayarwa Siriya ba waɗanda zata iya mafani dasu kan rikicin dake faruwa a ƙasar bane, kuma mun shafe shekaru masu yawa muna da kekkyawan alaƙa da Siriya. Bama goyon bayan ko wani bangare, saboda haka zai iya jefa ƙasar cikin yaƙin basasa.
Duka sassan na Rasha da Tarayyar Turai sun amince da shirin tsohon babban jami'in MDD Kofi Annan, shine zai taimaka wajen kawo ƙarshen rikicin na Siriya idan ya samu goyon bayan da ya dace. Har ila yau, matsalolin samar da makamashi tsakanin Rasha da Turai na cikin abubuwa da suka mamaye zaman taron na sassan biyu, kuma Shugaban ƙasar ta Rasha Vladimir Putin, ya yi ƙarin bayani kan abunda ke faruwa:
Makashin da muke turawa Jamus daidai wanda aka buƙata ne, saboda babu ƙarin buƙata da aka nema. Dukkanin sassan nada cin gashin kai, kuma dogaro da juna zai taimaka wajen samun daidaito kan makamashi tsakanin dukkanin bangarorin.
Taron na Kungiyar Tarayyar Turai da Rasha nada nufin warware banbance banbance da ake samu tsakanin sassan biyu.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita. Usman Shehu Usman