Rasha da Najeriya sun kulla yarjejeniyar makamai
August 25, 2021Talla
A sanarwar da ta fito daga ofishin jakadancin Najeriyan da ke birnin Moscow, ta ce, Rasha za ta taimaka da duk wasu fasahohi da ake bukata don ganin Najeriya ta iya murkushe Kungiyar Boko Haram da ta hana zaman lafiya a arewacin kasar.
Sanarwar ba ta fadi adadin kudin da za a kashe ba, sai dai ta ce, tun a yayin wata ganawa a tsakanin shugabanin kasashen biyu a shekara 2019, Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna sha'awar kula wannan yarjejeniyar, amma yanzu ne aka yi nasarar kulla yarjejeniyar a hukumance