SiyasaTarayyar Rasha
Rasha ta gargadi Amurka a kan kai hari a kan Iran
June 19, 2025Talla
A cikin wata sanarwa da ta bayyana kakakin diflomasiyyar Rasha Maria Zakharova ta ce ba za su laminta ba.
"Muna so mu gargadi Washington game da duk wani tsoma baki na soja a cikin wannan yanayin, wanda zai iya zama izgili na hatsarin gaske da zai janyo mummunar sakamakon da ba a zata ba.''
Jami'ar diplomasiyyar ta Rasha ta bayyana haka ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka DonaldTrump ya ce bai kawar da kai wa Iran hari ba.