Ranar 28 ga Afrilu ne za a gudanar da zabe a kasar Kanada
March 24, 2025Tsohon gwamnan babban bankin Kanada Mark Carney wanda ya maye gurbin Justin Trudeau ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin firaministan Kanada a tsakiyar wannan wata na Maris 2025. Sabon firaministan ya yi kiran da a gudanar da zaben gaba da wa'adi a ranar 28 na watan Afrilun dake tafe. Carney, mai shekara 59 a duniya, ya zama firaminista a daidai lokacin da Kanada ke fuskantar tarin kalubale daga makwabciyar kasar Amurka ciki kuwa har da na rikicin tattalin arziki.
Karin bayani: Ana zaben sabon shugaban jam'iyyar mai mulkin Kanada
Mark Carney wanda ya nemi shugabar rikon hadin kan kasa Mary Simon da ta rusa majalisa da ma kiran gudanar da zabe a karshen watan Afrilu, kuma ta amince, ya ce kasarsu na fuskantar kalubalen da ba su taba ganin irinsa ba, kuma ya ce ba za su taba bada kai domin bori ya hau ba. Carney ya kara cewar: "Ina neman hadin kan al'ummar Kanada su yi hakuri da juriya, domin za mu kawo karshen wannan matsalar. Na san akwai tarin abubuwan da kasarmu ke bukata, na farko dai a sake tabbatar da cin gashin kanta, a sake gina ta da kuma hada kan al'umma, shi yasa nake neman amincewarku."
Btutuwan da suka mamaye yakin neman zabe
A jawabinsa yayin kaddamar da yakin neman zabe a hukumance, madugiun adawa Pierre Poilievre dan jam'iyyar Conservatives ta yan mazan jiya ya ce lokaci ya yi da za su saka kasarsu a gaba. Ya ce: "A karon farko ya kamata mu saka kasarmu a sahun farko don samar da canji. Wannan sabuwar gwamnatin za ta rage muku harajin da kuke fama da sh,i za ta yi aiki tukuru don ganin ta samar da gidaje, kuma mu tsaya tare don mu yaki duk wasu matakan Donald Trump a kan kasarmu"
Baya ga Batun Trump da ke ci wa al'ummar Kanada da yawansu ya haura miliyan 40 tuwo a kwarya, matsalolin cikin gida da suka hada da tsadar rayuwa, na 'yan ci-rani na zama wani babban al'amari da ke sahun gaba a yakin neman zaben da za a gudanar. Sai dai tagomashin dan takarar jam'iyyar Liberal da ba su da rinjaye a majalisa na karuwa a tsakanin al'ummar Kanada. Masu sharhi a kan al'amuran siyasar kasar na cewar zaben ya yi kusa, saboda haka ba za a iya tantance komai ba.
Karin bayani: Trump ya sha alwashin karin kaso 50 na haraji kan Kanada
Masanin kimiyar siyasa Felix Mathieu ya ce: " A yanzu haka da kamar wuya a yi hasashen abin da zai faru a wannan zaben, amma dai tabbas zabe ne da za a sanya ido a kan shi da kuma ake sa ran ganin karuwar masu kada kuri'a". Sai dai shugaban Amurka ya nuna halin ko in kula ga wanda zai yi nasara a zaben na Kanada.