Rahoton kan saɓanin da aka fara samu tsakanin gwamnatin Najeriya da INEC
April 5, 2011Talla
A Najeriya al'umar ƙasar musamman yan siyasa da masu fafutukar kare mulkin dimokradiyya sun fara maida martani a game da rahotannin cewa gwamnatin na matsawa shugaban hukumar zabe Farfesa Attahiru Jega ya sauya tsarin zaɓɓukan ƙasar ko kuma ya sauka daga muƙaminsa. Wakilinmu daga Abuja Uwais abubakar Idris ya aikomana da rahoto.Sannan kuma daga nan Bonn Abdullahi Tanko Bala ya tuntuɓi Dr Garba Umar Kari manazarci kan al'Amuran siyasa kuma malami a jami'ar Abuja domin jin yadda suke kallon wannan al'amari
Mawallafi:Uwais Abubakar Idris
Edita : Abdourahamane Hassane