Tun bayan ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar Tarayyar Turai wato EU, masu fashin baki ke ganin cewa an dai raba gari ne tsakanin bangarorin biyu, amma akwai kalubale a gaba.
Tarayyar Turai ta yi rashin mamaba guda.Hoto: Getty Images/C. Furlong
Talla
Bayan da al'ummar Birtaniya suka kada kuri'ar raba gardama tare da zabar ficewa daga cikin kungiyar Tarayyar Turai wato EU, alamu ke nuni da cewa bangarorin biyu ba su shirya wa abin da ka iya biyo baya ba, in har Birtaniyan ta fice daga kungiyar ta EU.