Qatar da Masar na jiran ra'ayin Isra'ila kan yakin Gaza
August 19, 2025Kasashen Qatar da Masar da ke shiga tsakani a rikicin Gaza, na ci gaba da dakon jin ra'ayin Isra'ila kan shirin dakatar da yakin, bayan da kungiyar Hamas ta amince da sabbin sharuddan da ke cikin wannan yarjejeniya a ranar Litinin.
Kafar yada labaran Masar ta Al-Qahera News mai alaka da gwamnati, ta rawaito cewa sharuddan sulhun yakin sun kunshi tsagaita wuta ta tsawon kwanaki 60 a zangon farko, sai sakin wasu fursunonin yaki da Hamas ta yi garkuwa da su, da kuma sako wasu Falasdinawa da ke hannun Isra'ila, haka zalika da barin kayan agaji shiga yankin Gaza.
Karin bayani:Menene ra'ayin Isra'ilawa kan yaki da Hamas?
Amincewar Hamas na zuwa ne a daidai lokacin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke shan matsin lamba daga gida da ketare, kan janye muradinsa na yunkurin mamaye Gaza baki-daya da karfin bindiga.