Putin zai gana da Zelensky a matakin karshe na tattaunawarsu
July 25, 2025Da yake ganawa da manema labarai, Mista Peskov ya ce taron koli wanda shi ne mataki na karshe da za a cimma kwakwarar matsaya tare da masu shiga tsakani, ba zai yiwu a cikin hanzari ba.
Kakakkin fadar ta Kremlin ya kara da cewar baya ganin yiwuwar hakan a watan Augusta kamar yadda mahukuntan Kyiv suka bukata.
Ukraine dai ta ce ana bukatar taron shugabannin ne domin cimma nasara a yunkurin kawo karshen yakin dake tafiyar hawainiya.
Bangaorin biyu sun gudanar da taruka a tsakaninsu har saui uku karkashin jagorancin Turkiyya tun a tsakiyar watan Mayu.
Shugaban Amurka Donald Trump wanda a baya ya sha tatatunawa da Putin a kan wannan batun , ya sha alwashin kakabawa Rasha sabbin takunkumai da duk wata kasa dake goyon bayanta muddin aka gaza cimma yarjejeniya nan da watan Satumba.
Karin bayani:Putin da Zelensky ba za su halarci taron sulhu a Istanbul ba