Rasha ta gargadi sojin Turai kan shiga Ukraine
September 5, 2025Talla
Putin ya ce matakin da kungiyar EU ke shirin dauka tamkar halatta farmaki ne ga rundunarsa. Ya kara da cewa girka sojojin waje a Ukraine yayin da rikicin ke gudana zai iya haifar da martanin soja daga Moscow.
Gwamnatin Rasha ta yi gargadin cewa duk wani shiri na jibge sojojin waje a Ukraine zai warware duk wani yunkurin samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Wannan jawabin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kasashen Turai, karkashin jagorancin Birtaniya da Faransa, suka sha alwashin ba da tabbacin tsaro ga Ukraine, wanda ya hada da yiyuwar tura dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen duniya a nan gaba.