Putin ya ba da shawarar Ukraine ta dawo karkashin MDD
March 28, 2025A lokacin da yake ziyara a yankin Murmansk da ke arewa maso yammacin Rasha, shugaba Vladimir Putin ya ce zai iya tattaunawa da Amurka har ma da kasashen Turai da kuma sauran kasashe abokan hulda karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya, don kafa hukumomin rikon kwarya da za su tafiyar da lamuran Ukraine.
Mista Putin ya kara da cewa, kafin a tattauna batun samar da zaman lafiya a Ukraine, yana da mahimmanci a girka halastattun hukumomi na dimokuradiyya da zu wakilci Kiev a zaman da za a yi na sulhu.
Karin bayani: Macron na jagorantar gangamin tallafawa Ukraine
Wadannan kalamai na Putin na zuwa ne a daidai lokacin da kawayen Ukraine na Turai suka kammala wani taro a birnin Paris na Faransa a ranar jiya Alhamis, inda suka tattauna kan samar wa Ukraine da garkuwa a fannin tsaro. A yayin taron kasashen Burtaniya da Faransa sun gabatar da shirin aike wa da dakarun tabbatar da tsaro a Ukraine nan gaba, don kare al'ummar kasar daga hare-haren Rasha.