Putin da Trump sun shata hanyar wanzar da lafiya a Ukraine
March 18, 2025Tattaunawar da ta gudana ta wayar tarho tsakanin Vladimir Putin na Rasha da Donald Trump na Amurka kan shirin wanzar da zaman lafiya a Ukraine ta kammala, ba tare sassan biyu sun wani cikakken bayani ba. Amma dai fadar mulki ta Kremlin ya danganta tattaunawar da cewa yana cike da bayanai na gaskiya, yayin da fadar White House ta ce Trump da Putin suna son tsagaita wuta don a gudanar da aiki tono makamashi da samar da ababen more rayuwa.
Dama dai tun da farko, shugaban Amurka, ya bayyana cewar a shirye yake ya tattauna da Putin kan yankunan Ukraine da ya mamaye, lamarin da ke matukar damun fadar mulki ta kyiv. Sai dai ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Sybiga ya dage kan cewar dole ne Moscow ta amince da shirin tsagaita wuta na wata guda ba tare da gindaya wani sharadi ba.