Putin da Modi da wasu shugabanni na halarta taro a China
August 31, 2025Shugaba Xi Jinping na kasar China, ya karbi bakuncin shugabannin Rasha da Indiya da wasu na kusan kasashe 20 na yankin Turai da Asiya a birnin Tianjin, a wani taron koli da ke gudana har zuwa ranar Litinin, domin karfafa matsayinta a harkokin diflomasiya.
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya isa kasar ne a yau Lahadi tare da manyan jami'an gwamnati da wakilan fannin kasuwanci.
Ana kuma sa ran shugaban na China zai gana da shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, da shugaban Iran Masoud Pezeshkian, domin tattauna batun yakin Ukraine da shirye-shiryen nukiliyar Tehran.
A gefe guda, Xi ya gana da shugabannin Maldives da Azerbaijan da Kyrgyzstan da shugaban Belarus, Alexander Lukashenko.
Har ila yau, ya gana da Firaministan Indiya, Narendra Modi, wanda ke ziyara ta farko a China tun 2018.