Rasha ta amince da sulhu da Ukraine bisa manufa
March 13, 2025Shugaba Vladimir Putin ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Moscow, inda ya ce tilas a yi aiki kan matakan cimma yarjejeniyar misali matakan da za a dauka idan aka karya ka'idojin yarjejeniyar. Ya kara da cewa wani abu kuma da ya kamata ayi la'akari da shi kan batun sulhun shi ne, ko ukraine za ta iya yin amfani da kwanaki 30 na tsagaita wutar wajen ci gaba da kara karfin dakarunta. A cewarsa kafin cimma batun zama kan teburin sulhun kuma tilas ne sojojin Ukraine da ke yankin Kursk da a yanzu dakarunsa suka yi musu kawanya, su yanke shawarar ajiye makamansu ko kuma mika wuya. A hannu guda kuma Putin din ya ce akwai yiwuwar shimfida bututun iskar gas a Turai ganin cewa tana bukatar iskar gas din Rashan mai rahusa, idan har Moscow da Amurka suka cimma yarjejeniya kan huldar makamashi a tsakaninsu.