Paparoma Francis ya fito bainal jama'a
April 6, 2025Shugaban darikar Katholika na duniya Paparoma Francis, ya yi wa mabiya fitar ba zata a dandalin St. Peters a wannan Lahadi, a lokacin da ake gabatar da addu'o'i ga marasa lafiya da jami'an kiwon lafiya.
Wannan ne karo na farko da Paparoman ke fita bainal jama'a a fadar Vatikan, tun bayan barin sa asibiti makonni biyu da suka gabata, inda ya yi fama da matsanciyar jinyar cutar numfashi.
Paparoma ya daga wa mabiya hannu yayn da su mabiyan ke sowa lokacin da yake kewayawa bisa kekensa na marasa lafiya.
Muryarsa dai ta yi karfi fiye da lokacin da yake kwance a asibitin Gemelli, musamman a ranar 23 ga watan jiya da aka sallame shi.
An dai ga Paparoma Francis mai shekaru 88 da wani bututun shakar numfashi, wanda fadar Vatikan ta ce sannu a hankali za a cire masa shi.