Pakistan ta yi gwajin wani makami mai linzami
May 4, 2025Talla
Pakistan ta yi gwajin wani makami mai linzami daidai lokacin da dangantaka tsakaninta da Indiya ke kara tsami, bayan hari mai munin da aka kai kan wasu Indiyawa 'yan yawon shakatawa a yankin Kashmir cikin watan jiya.
Rundunar soji a Pakistan ta ce makamin mai linzami ya yi tafiyar kilomita 450 daga in da aka harba shi.
Hukumomi a Islamabad sun ce wannan wani aiki ne na musamman da dakarun kasar ke yi domin tabbatar da lafiyar makamansu a wannan lokaci.
Babu dai wani martani daga bangaren kasar Indiya a game da abin da Pakistan din ta yi, sai dai kuma ta dora wa Pakistan laifin kisan 'ya'yanta da dama da aka yi a garin Pahalgam a ranar 22 ga watan jiya, zargin kuma da Pakistan din ke musantawa.