Pakistan ta kori miliyoyin bakin haure 'yan Afghanistan
March 31, 2025Kasar Pakistan ta shirya tsaf domin korar 'yan asalin Afghanistan sama da miliyan uku da ke babban birnin kasar da keyawe, bayan hukumomin kasar ta Pakistan sun basu wa'adin ficewa daga kasar daga wannan rana ta Litinin 31 ga watan Maris 2025.
Karin bayani: Jamus: Tisa keyar 'yan Afghanistan gida
Hukumomin Pakistan sun kaddamar da korar miliyoyin bakin haure da ke zaune a kasar ba bisa ka'ida ba, musamman a biranen Islamabad da Rawalfindi, wanda hakan ya haifar da martani daga gwamnatin Taliban da kuma Majalisar Dinkin Duniya.
Karin bayani: MMD na taro a Qatar kan makomar Afghanistan
Dubun dubatar 'yan Afghanistan na zaune a Pakistan da Amurka tun bayan kafa gwamnatin Taliban a 2021, duk da cewa wadanda ke zaune a Amurkan na cikin wadi na tsaka mai wuya sakamakon matakan da gwamnatin Trump ke dauka na korar bakin haure.