SiyasaAsiya
Pakistan ta kakkabo jiragen yakin India biyar
May 7, 2025Talla
Sabon rikicin dai ya samo asali ne tun lokacin da India ta yi zargin cewa Pakistan ta halaka wasu 'yan yawon bude idon kasarta akalla 26 a ranar 22 ga watan Afrilu a yankin Kashmir dá ke karkashin kulawar India. Hukumomin Pakistan sun musanta hannu a harin da aka kai yankin na Kashmir.
Karin bayani:Wani harin kwanton bauna ya hallaka sojojin India a Kashmir
Babban Hafsan Tsaron Pakistan ya ce fararen hula akalla 26 suka mutu yayinda wasu da dama suka jikkata a gumurzun da kasashen biyu suka yi a wannan rana.
Karin bayani:Iran na kokarin sasanta Indiya da Pakistan
India da Pakistan dai sun shafe shekaru suna gwabza yaki daga lokaci zuwa lokaci tun bayan samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallakar Burtaniya a 1947.