Pakistan ta ceto fasinjoji 190 da aka yi garkuwa da su
March 12, 2025Pakistan ta kaddamar da wani gagarumin farmaki na ceto fasinjojin jirgin kasa da mayaka suka yi garkuwa da su a tsaunukan Kudu maso yammacin kasar. Majiyoyin tsaro sun ce an yi nasarar kubutar da fasinjoji 190 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, tare da halaka 'yan bindiga 30 a arangama da suka yi. Sai dai, fiye da fasinjoji 450 ne ke cikin jirgin lokacin da mayakan suka yi kwace shi, kuma ana ci gaba da tsare adadi mai yawa na fasinjojin. Amma, wadanda da aka sako sun bayyana cewar sun yi tafiya na sa'o'i a cikin tsaunuka kafin su kai ma tudun mun tsira.
Wasu ‘yan bindiga ne suka kai harin bam a wani bangare na layin dogo tare da kai farmaki kan jirgin a jiya da Yamma a lardin Balochistan mai iyaka da Iran da Afghanistan, inda ake ci gaba da samun karuwar hare-haren ‘yan aware. Kungiyar 'yan tawayen Baloch - kungiyar BLA ce ta dauki alhakin kai harin