Olaf Scholz ya caccaki manufofin Merz na bakin haure
January 29, 2025Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya caccaki yunkurin kulla kawancen siyasa da jam'iyyar adawa ta 'yan mazan jiya ta CDU ke shirin yi da takararta ta masu kyamar baki Alternative Für Deutschland (AfD) a zaben gabanin wa'adin da ke tafe a watan gobe.
Karin bayani: Zaben Jamus 2025: Elon Musk na fatan nasara ga AfD
Olaf Scholz ya bayyana cewa kulla irin wannan kawance kan batun bakin haure da jam'iyyun adawar biyu ke son yi a tsakanin masu kyamar baki da jam'iyyar tsohuwar shugabar gwamnati Angela Merkel babban kuskure ne da ba zai yi a yafe shi ba.
Tun bayan yakin duniya na biyu, jam'iyyun siyasar Jamus masu rajin kare dimukuradiyya na samun masalaha da junansu ne a majalisar dokoki, saboda hakan ba za mu taba ci a akushi guda da masu tsananin kyamar baki ba, a cewar Scholz.
Karin bayani: Jam'iyyar SPD ta damka wa Scholz tikitin takara a zaben gabanin wa'adi
Dan takarar jam'iyyar SPD da ke jagorantar kawancen masu mulki da ya ruguje, na zargin dan takarar CDU/CSU Friedrich Merz, da yunkurin yi wa masalahar da ake cimmawa a tsakanin jam'iyyun siyasar kasar ne karan-tsaye don lashe zabe ko ta halin kaka.
Ko a wannan Laraba, jam'iyyar CDU/CSU sun gabatar da wani sabon kudri da ke shirin daukar zazzafan matakai kan bakin haure, ciki har da dakatar da su a bakin iyaka ko da kuwa masu neman mafaka ne, kuma tuni ma dai ya samu goboyn bayan jam'iyyar AfD