SiyasaAfirka
NIMET ta yi hasashen ambaliyar ruwa a jihohi 21 a Najeriya
August 6, 2025Talla
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya NIMET ta yi hasashen cewa jihohi 21 daga cikin 36 ka iya fuskantar matsalar ambaliyar ruwa a 'yan kwanaki masu zuwa.
Karin bayani:Najeriya: Ambaliya na ci gaba da lakume rayuka
Hukumar NIMET ta sake sanya jihar Neja daga cikin jihohin da ke da hadari ta bangaren fuskantar ambaliyar ruwa, inda ko a watan Mayun wannan shekara aka samu mummunar ambaliyar ruwa wanda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 200.
Karin bayani:NIMET ta yi hasashen tsananin zafi a Najeriya
A shekara ta 2022, ambaliyar ruwa ta halaka mutane sama da 500 a Najeriya, yayin da mutane sama da miliyan 1.4 suka rasa muhallansu, ko a daminar shekarar da ta gabata ta 2024 sama da mutane 300 ne suka mutu a jihohi 34 daga cikin 36.
..