Nijar za ta karbi bakin hauren da aka koro daga Aljeriya
May 18, 2025Gwamnan jihar Agadez, Ibrah Boulama ya ce, Nijar ta shirya karbar bakin hauren ne kimanin 4,000 tare da hadin gwiwar hukumar kula da kaura ta duniya IOM. An dai tsara gudanar da wannan shiri ne daga yanzu zuwa watan Yulin wannan shekarar. Jami'an 'yansanda da suke garin Assamaka da ke kusa da iyakar kasar sun ce kawo yanzu bakin haure kimanin 6,000 ne suka iso, adadin da ya sanya matsugunni da IOM ta bayar ya cika.
Karin bayani:Nijar: Bai wa bakin haure damar wucewa Turai
Tun a shekarar 2014 ne dai, ake koro bakin hauren 'yan asalin Nijar da ma wasu kasashen Afirka daga Aljeriya, inda nan ne ke zama matattara ta wadanda ke neman tsallakawa turai ta barauniyar hanya. Alkalumma sun yi nuni da cewa, a bara gwamnmatin Aljeriya ta koro bakin haure sama da 31,000 zuwa Nijar.