Nijar za ta kama Gaddafi in ya shiga ƙasar
September 9, 2011Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bada tabbacin cewa za ta martaba umarnin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, hakan yana nufin idan kanal Gaddafi ya taka ƙasar za a kama shi kuma a miƙa shi. Daraktan majalisar zartas wan gwamnatin jamhuriyar Nijar Massa'udu Hassumi ya fadawa kamfanin dillalcin labarai na Reuters cewa, Nijar ɗaya ce daga ƙasashen da suka sanya hannu a kotun hukunta masu aikata manyan laifuka, don haka idan Gaddafi da muƙarrabansa da ake nema suka shiga ƙasar sun son abinda zai same su. Massa'udu Hassumi yace Nijar ƙasa ce mai mutunta haƙƙin bil'adama, amma dole ta kare nauyin da ke kanta na ƙasa da ƙasa. Ƙasar Birtaniya da ƙawayen ta waɗanda suka tallafa don kifar da gwamnatin Gaddafi, sun buƙaci ƙasashen da suka sa hannu a yarjejeniyar kotun ƙasa da ƙasa mai hukunta manyan laiku, da su suka kama kuma su miƙa Gaddafi ga kutun na ƙasa da ƙasa da ke da zama a birnin Huge. A halinda ake ciki kuwa an bada rahoton cewa wata tawaga mai mutane 14 ɗauke da manyan jami'an Gaddafi ta isa birnin Agades da ke arewacin jamhuriyar ta Nijar.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu